Wasu kungiyoyin matasan Musulmai da malamai sun shirya zanga-zanga don nuna bacin ransu kan yadda ake zargin an yi wa wata mata fyade a wani masallaci da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Jaridar Aminiya ta ruwaito.
Bayanai sun nuna matar na sanye da Nikabi lokacin da ta gamu da iftila’in.
Kungiyoyin masu ruwa da tsaki na Musulmai ne dai suka shirya zanga-zangar a ranar Litinin.
Aminiya ta gano cewa an gano wanda ake zargi da aikata fyaden da ne ga wani fitaccen Shugaban Kungiyar Direbobi.
Masu zanga-zangar dai na bukatar a kama tare da gurfanar da mutumin ne don ya fuskanci fushin hukuma.
A wani labarin kuma, wata kungiya mai kare muradun Musulmai mai suna MPAC, ta bayyana takaicinta da fyaden, tare da yin kira da a hukunta wanda ya aikata shi.
Sai dai a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Disu Kamor, ya fitar ranar Talata, ya ce tuni ’yan sanda suka kama wanda ake zargin.
Sanarwar ta ce, “Wannan abin da aka yi wa ’yar uwarmu cin fuska ne kuma ba za mu lamunta ba. Ba yadda za a yi kowace al’umma ta bari ana wulakanta matanta, kuma ana cin zarafin masu kamala.
“Saboda haka, muna kira da a gaggauta gurfanar da wanda ya yi wannan danyen aikin tare da zartar masa da tsattsauran hukuncin da ya dace da shi.”