Jihar Ribas - Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers, ya yi watsi da rade-radin cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) gabanin babban zabe na 2023. Legit.ng ya wallafa.
Gwamnan jihar Ribas ya ce ya ci gaba da zama dan jam’iyyar PDP da bai tuba ba duk da yadda APC ke goyon bayan sauya shekar mulki zuwa kudu.
Sanarwar da aka fitar a shafin Gwamna Wike na Facebook na nuni da cewa ya fadi haka ne a wajen taron Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar Ribas karo na 114 a Fatakwal a ranar Litinin, 20 ga Fabrairu.
“Ni ba dan APC ba ne kuma ba zan kasance ba. Amma, sun sa na gane cewa su ne jaruman kasar nan.
“Gwamnonin jam’iyyar APC sun fito sun ce shugabancin kasarnan ya koma kudu".inji Wike.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI