Yanzu-Yanzu: Gobara ta tashi a hedkwatar yan sandan jihar Kano, ofisoshi sun kone


An yi asarar dukiya da kaya na miliyoyin naira sakamakon gobara da ta faru a hedkwatar rundunar yan sanda da ke Bompai, karamar hukumar Nasarawa, jihar Kano.

Wani shaidan gani da ido ya fada wa Daily Sun cewa gobarar ta fara ne misalin karfe 2 na ranar Asabar, ya kara da cewa ta shafi ofishin Provost har zuwa ofishin mataimakin kwamishinan yan sanda.

Daily Trust ta rahoto cewa gobarar ta tashi ne daga ofishin Provost sannan ta bazu zuwa sashin kudi, dakin taro, ofishin kakakin yan sanda, ofishin mai tallafawa kwamishina (bangaren mulki), ofishin mataimakin kwamishina (bangaren mulki) da wasu wuraren.

A cewar shaidun gani da ido, amma gobarar ba ta shafi sabon ofishin kwamishinan yan sanda da wasu gine-gine da ke kallon ofishin ba.

Ana kyautata zaton cewa gobarar ta kona takardu da dama, amma babu rahoton rauni ko rasa rai sakamakon gobarar, kawo yanzu.

Kawo yanzu ba a san dalilin tashin gobarar ba domin ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ba, don ji ta bakinsa.

Amma, jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun samu nasarar kashe wutan, kamar yadda aka gano suna aiki tukuru yayin da jami'an tsaro suka zagaye hedkwatar yan sandan.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN