‘
Yan bindiga sun harbe ‘yan sanda 3 har lahira a Abakaliki ranar Asabar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, SP Chris Anyanwu, ya bayyana a ranar Lahadi a Abakaliki cewa an kashe ‘yan sandan ne a wata unguwa da ke kan iyaka tsakanin Ebonyi da jihar Enugu.
“Yan bindigar sun yi aiki ne a cikin motocin Sienna guda biyu, suka shiga shingen binciken ’yan sanda kuma suka bude wuta kan ‘yan sandan.
“Jami’an ‘yan sanda uku na ‘Operation Safer Highway’, sun samu munanan raunuka, kuma daga baya jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu,” in ji Anyanwu.