Yadda mota ta take mara lafiya ya mutu a harabar asibiti

Yadda mota ta take mara lafiya ya mutu a harabar asibiti


Wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Mallam Zubairu ya rasu bayan wata mota ta rutsa da shi a harabar asibiti
.

Zubairu wanda mazaunin garin Lamingo ne da ke karamar hukumar Jos ta Gabas ya ziyarci asibitin koyarwa na jami’ar Jos (JUTH) kan matsalar lafiya inda ya gamu da ajalinsa.

Wani dan uwa mai suna Abok wanda ya zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya bayan afkuwar lamarin, ya ce marigayin ya ziyarci asibitin ne domin a duba lafiyarsa.

Abok ya kara da cewa marigayi Zubairu yana kan hanyarsa ta fita daga asibiti sai wata mota ta rutsa da shi.

“Nakan kai shi asibiti domin duba lafiyarsa na yau da kullun amma bai kira ni ba a yau, sai aka ce min dansa ya kawo shi asibiti.

“Ya samu nasarar ganin likitan kuma yana kan hanyarsa ta zuwa tashar mota a cikin asibitin yayin da dansa ya bar shi ya samu babur da zai kai su gida.

“Abin takaici ya fadi yana tafiya sai wata mota ta bi shi kuma ya samu raunuka.

“Nan da nan aka garzaya da shi sashin gaggawa na asibitin domin a kula da shi amma cikin bakin ciki ya rasu,” inji shi.

Wani ma’aikacin asibitin da ya bayyana kaduwarsa da faruwar lamarin, ya bayyana marigayin a matsayin wani sananne a asibitin inda yake kai kayan lambu ga galibin ma’aikatan asibitin.(NAN)

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN