Yadda Jagororin PDP suka yi banza da Atiku yayin da ya zo kamfe a jihar Kebbi


Manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP na reshen jihar Kebbi sun kauracewa taron Atiku Abubakar na yakin zaben shugabancin kasa. Legit.ng ya wallafa.

Rahoton The Nation ya bayyana cewa da-dama daga cikin shugabannin PDP ba su je taron da aka yi a garin Birnin Kebbi a karshen makon da ya wuce ba.

Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya da abokin takararsa watau Ifeanyi Okowa sun ci karo da rikicin cikin gidan da ake yi a jihar Kebbi.

Abin da ya jawo sabanin shi ne ana zargin jam’iyyar adawar da fifita wasu daga cikin tsofaffin ‘ya ‘yan APC da suka sauya-sheka a kan asalin ‘ya 'yan PDP.

Wadanda suka sha kashi a yakin neman zaben APC sun samu tikitin takara daga dawowarsu PDP. Rahoton ya ce wannan ya jawo ake ta shari’a a kotu.

Su wa suka halarci taron?

Manyan ‘yan PDP da suka je taron kamfen da aka yi sun hada da tsofaffin Ministoci irinsu, Samaila Sa’idu Samabawa, Kabiru Tanimu da kuma Buhari Bala.

Jagororin PDP

Laftana Janar Ishaya Bamayi (retd.), Manjo Janar Bello Sarkin Yaki (retd.), da ‘yan takara; Ibrahim Manga, Sani Bawa, Haruna Saidu sun halarci gangamin.

Baya ga wadannan, akwai jiga-jigan PDP da-dama ba su taka kafarsu zuwa wajen yakin neman zaben da aka shirya a filin sukuwa da ke birnin Kebbi ba.

Zan bude iyakoki - Atiku

Independent ta rahoto cewa Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin bude duka iyakokin kasar nan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta rufe a 2019.

Da yake bayani a wajen taron, Atiku Abubakar ya ce a matsayinsa na tsohon jami’in kwastam, ya fi sauran masu neman takara fahimtar sha’anin iyakoki.

‘Dan takaran PDP ya na zargin rufe iyakokin da aka yi ya takaita kasuwanci da jawo rashin aiki.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN