Wata mata mai shekara 50 ta shake tsohuwa mai shekara 60 har Lahira a jihar arewa


Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wata mata mai suna Amina Guguwa mai shekaru 50 da haihuwa bisa zargin kashe matar aure.

Kakakin rundunar, SP Ahmed Mohammed Wakil, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, 5 ga watan Janairu, 2023, ya ce wanda ake zargin ta shake mariganyar har lahira.

Sanarwar ta kara da cewa, "Bayanan da hukumar ta samu sun nuna cewa a ranar 1 ga watan Janairun 2023, Amina Koli (Marigayiya) 'f' mai shekaru 60 a garin Miya ta mu bayan an shake ta har lahira bayan wata arangama da suka yi.

“Amina Guguwa, wadda ake zargin ta yi amfani da karfi wajen shake wuyanta , sakamakon haka ta mutu nan take.

 “A lokacin da aka samu rahoton, an tura wata tawagar jami’an tsaro, inda suka garzaya zuwa wajen da lamarin ya faru, kuma suka dauki gawar zuwa babban asibitin Ganjuwa domin duba lafiyar ta, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar ta.

 "Ana ci gaba da gudanar da bincike, bayan haka kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya."  PPRO ya kara da cewa.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN