Tinubu ya fara yunkurin samun kuri'u daga 'yan Najeriya, yana shirin yin kawance da PDP, Labour Party

Tinubu ya fara yunkurin samun kuri'u daga 'yan Najeriya, yana shirin yin kawance da PDP, Labour Party


Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC na shirin kulla kawance da kananan jam’iyyun siyasa a fadin kasar nan. Legit.ng ta wallafa.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, wannan kawance da wasu jam’iyyu zai taimaka wa jam’iyyar APC wajen bunkasa damar dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, ya lashe zaben 2023.

An tattaro cewa jam’iyyar PCC na fatan yin hakan zai jawo jam’iyyun daukar Tinubu a matsayin ma’auni gabanin zabe.

A ranar Litinin, 9 ga watan Janairu ne tsohon gwamnan jihar Legas ya gana da gwamnonin jam’iyya mai mulki domin magance wasu matsalolin da suka taso a tsakanin mambobin kungiyar.

Babban jigo a jam’iyyar APC ya tabbatar da shirin jam’iyyar na kawance

Wani tsohon dan majalisa, Adesoji Akanbi da ke zama mamba a jam’iyyar APC ta PCC ya tabbatar da cewa jam’iyya mai mulki tana kallon sauran manyan jam’iyyu kamar PDP, New Nigeria Peoples Party da Labour Party don kulla yarjejeniyoyin da suka dace kafin zaben.

Akanbi ya kara da cewa ana ci gaba da tattaunawa da kananan jam’iyyu a jihar Oyo.  Ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar APC na sauran jihohin da su yi amfani da wannan dabarar.

Yace:

“Muna tuntubar mambobin Accord (Party) da Social Democratic Party da sauran jam’iyyun siyasa domin su zabi Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa.

“Neman masu sauya sheka (zuwa APC) ya makara a yanzu;  wanda ba zai yi aiki ba, wato kamar bata lokaci ne.  Hakan na iya faruwa da son rai.  Abin da muke sayar musu shi ne samfurin – Bola Ahmed Tinubu – na shugaban kasa.

"Ya kamata su fito su ba shi goyon baya a kan wannan dalili don su samu shugaban da zai iya kawowa."

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN