Sarkin Kano ya kara yin aure, ya auri Hauwa’u

Sarkin Kano ya kara yin aure, ya auri Hauwa’u


Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya auri mata ta biyu, Hauwa’u Adamu Abdullahi Dikko. Jaridai Aminiya ta wallafa.

An daura auren ba tare da taron jama’a ba a ranar Juma’a a gidan marigayi Jarman Kano, Farfesa Isah Hashim, da ke unguwar Nassarawa G.R.A a Jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa amaryar ta fito ne kai daga zuriyar Malam Jamo, wanda dan uwa ne ga marigayi Sarkin Kano, Ibrahim Dabo.

An fara batun shirye-shiryen auren tsakanin Sarkin mai shekara 60 a duniya da kuma tsohuwar masoyiyarsa a shekarar da ta gabata.

An bayyana cewa sarkin ya auri mace daya ne sama da shekara 30 kuma suna da ‘ya’ya hudu a tsakaninsu.

Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani Ibrahim, ne ya wakilci ango a matsayin waliyyi a wajen daurin auren, yayin da Alhaji Shehu Hashim, ya kasance waliyyin amarya.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa Aminiya cewa an biya Naira 500,000 a matsayin sadaki kuma an kai amarya gidan mijinta a ranar Asabar.

“An daura auren ba tare da sanarwa ba. Ko da yake sarki ya yi gaggawar dawowa daga Maroko. An kai amarya Fada a ranar Asabar.”

Aminiya ta ruwaito cewa Makaman Bichi, Alhaji Isyaku Umar Tofa, Sarkin Dawaki Mai Tuta na cikin wadanda suka halarci daurin auren.

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN