Rana ta bace: Yan bijilanti sun halaka wani mai garkuwa da mutane a Kano
A daren jiya ne aka yi musayar wuta tsakanin tawagar Ali Gomon da ta ƴan Bijilanti, lokacin da masu garkuwar suka yi yunƙurin yin awon gaba da wani ɗan kasuwa Alhaji Ɗahiru.
Shugaban Æ´an Bijilanti na Sumaila Alhaji Wada Muhammad ya shaida wa Freedom Radio cewa sun yi amfani da bindiga, an kuma É—auki lokaci ana bata-kashi a tsakaninsu kafin samun nasara a kan masu garkuwar.