Malamin addini ya yi garkuwa da kansa ya karbi kudin fansa N600,000 daga hannun mambobin wajen ibada

Malamin addini ya yi garkuwa da kansa ya karbi kudin fansa N600,000 daga hannun mambobin wajen ibada


Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Filato sun kama wani Fasto mazaunin garin Jos bisa laifin yin garkuwa da kansa da kuma neman kudin fansa a hannun ‘yan cocinsa
.

An kama Albarka Bitrus Sukunya ne tare da abokan aikata laifi biyo bayan rahotannin sirri bayan da mabiya cocin suka biya kudin fansa N600,000 domin a sako malamin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, 11 ga watan Janairu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta sake bankado munanan aika-aikar da wani Fasto mai suna Albarka Bitrus Sukuya ‘m’ na Jenta Apata, Jos ya aikata wanda a lokuta da dama ya yi garkuwa da kanshi tare da ‘yan abokan aikata laifi kuma ya karbi kudin fansa daga masu tausayawa ’yan cocinsa.

“Bayan kitsa sace kansa da ya yi a ranar 14/11/2022 da 30/11/2022 inda masu goyon bayansa suka biya Naira Dubu Dari Hudu (N400,000) da Naira Dubu Dari Biyu (N200,000) a matsayin kudin fansa kafin sakinsa, abubuwan da suka faru sun jawo tuhuma.


“Ta hanyar samun bayanan sirri, DPO na Nassarawa Gwong, CSP Musa Hassan, ya gayyaci Malamin, kuma aka fara bincike nan take, a binciken da ake yi, an gano cewa wanda ake zargin yana hada baki da ‘yan kungiyarsa wajen yin garkuwa da kanshi da kuma zamba don ya karbi kudin fansa.

“Da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin aikata laifin kuma ya ambaci wadannan mutane a matsayin wadanda suka taimaka masa: (1) Baruk Mailale, (2) Nathaniel Bitrus duka mazan Yelwan Zangam da ke Jos-arewa da (3) Aye na Jalingo, Jihar Taraba.

“Wanda ake zargin ya ci gaba da bayyana cewa a ranar 04/01/2023 ya kona motoci guda biyu (Mercedes Benz da Toyota) da kuma wani keke da yake ajiye a harabar ECWA Bishara 3 Jenta Apata na abokan aikinsa wanda ya yi zargin cewa daya daga cikinsu ya tsane shi, yana nufin babban fastonsa.

“Sai dai jami’an ‘yan sanda reshen Nassarawa Gwong reshen Jos-arewa LGA sun kama mutum biyu (2) daga cikin wadanda ake zargin, Baruk Mailale da Nathaniel Bitrus yayin da ake kokarin kama Aye, mutum na uku da ake zargi.”

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN