Ko Majalisar dokokin jihar Kebbi za ta iya tsige Gwamna Bagudu?


Tun ranar 26 ga watan Janairu 2023, Majalisar dokoki na jihar Kebbi ta shiga takun saka da Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, lamari da ya bayyana sakamakon wata takarda da ta bulla da ya ja hankalin jama'ar jihar Kebbi dangane da abin da ke faruwa tsakanin bangarorin guda biyu. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Bayanai da ke kunshe a takardu da suke da asali da rigimar, an samo cewa yan Majalisar sun gagyaci Gwamna Bagudu ya bayyana a gabansu domin ya yi masu bayani yadda ya sarrafa wasu makuddan kudi da suka zarce Naira biliyan goma sha takwas N18bn.

Yan majalisar sun bukaci Gwamna Bagudu ya bayyana a gabansu ranar 27 ga watan Janairu domin yin bayani. Sai dai Kwatsam ranar 26 ga watan Janairu, lamurra sun canja, kuma mataimakin Kakakin Majalisar dokokin jihar tare da wasu yan Majalisar sun sanar da yin murabus daga mukamansu.

Ina aka kwana?

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa ana ci gaba da sasantawa tsakanin bangarorin guda biyu wanda ya hada da tuntuba a babban mataki na masu ruwa da tsaki a jam'iyar APC mai mulki a jihar Kebbi, da kuma wadanda ake ganin suna da martabar da za a saurare su wajen aiwatar da sulhu.

Me zai faru idan Gwamna bai amsa gayyatar Yan Majalisar dokokin jiharsa ba?

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa kundin tsarin mulki na Najeriya ya ba Majalisar dokokin jiha dama ta gayyaci Gwamna domin ya zo ya yi mata bayani idan an sami wani lamari da ke bukatar a fayyace shi domin warware sarkakiya game da lamarin da ya shafi jihar da jama'arta .

Sai dai wata majiya ta Sharia ta ce idan har Gwamna ya ki zuwa da gangan, kuma bai aika wani dalili da ya hana shi zuwa ko ban hakuri ba. Idan Majalisar ta dubi wannan a mahangar "babbar rashin da'a" watau GROSS MISCONDUCT, Majalisa zata iya tsige Gwamana a bisa wannan hurumi. Daga nan Majalisa za ta iya fara daukan matakan da suka wajaba bisa tsarin doka don aiwatarwa.

Daga isyaku.com

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN