Kayya jama'a: An kama mai siyar da karas yana Luwadi da almajiri, duba yadda ta faru

Kayya jama'a:  An kama mai siyar da karas yana Luwadi da almajiri, duba yadda ta faru


Hukumar yaki da ‘yan daba ta Zamfara ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata luwadi. Shafin ISYAKU.COM ya samo

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa Kwamitin ya kuma ce ya samu nasarar cafke wasu mutane shida da ake zargi da satar waya da kuma fashi da makami.

Shugaban kwamitin, Mista Bello Bakyasuwa, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Litinin a Gusau.

Bakyasuwa ya ce jami’an ‘yan sandan da ke yaki da ‘yan fashi sun kama daya daga cikin wadanda ake zargi da yin luwadi a unguwar Tudun Wada da ke Gusau babban birnin jihar.

“Wanda ake zargin ya amsa laifin aikata wannan mugunyar aiki tare da wani yaro dan shekara 7.

“Wani wanda ake zargi da yin luwadi, mai sayar da karas ma jami’an mu sun kama shi da laifin lalata wani yaro almajiri a cikin babban birnin Gusau.

"Wannan wanda ake zargin ya kware wajen jawo yaran almajirai musamman da karas su aikata munanan aiki da su," in ji shi.

A cewarsa, daga cikin mutane shida da aka kama bisa zargin satar waya da fashi da makami, an kama wasu ne a yayin wani gangamin yakin neman zaben gwamnan PDP da aka gudanar a garin Kaura Namoda kwanan nan.

“Wasu daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne a cikin birnin Gusau a hannun ‘yan sintiri dauke da muggan makamai da kuma zargin satar waya.

“Dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata laifin ne lokacin da muka yi musu tambayoyi,” ya kara da cewa.

Bakyasuwa ya ci gaba da cewa, duk wadanda ake zargin sun saba wa dokar zartarwa ta Gwamna Bello Matawalle mai lamba ll kan yaki da ‘yan daba, shaye-shayen kwayoyi da sauran laifuka masu alaka da su.

Ya ce za a mika wadanda ake zargin ga hukuma domin ci gaba da bincike.

Bakyasuwa ya yi kira ga iyaye da masu riko da kuma makarantun almajirai da su tabbatar da sanya ido sosai kan ‘ya’yansu.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bin kwamatin a kokarinsa na yaki da ‘yan daba da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar baki daya.

2 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. Dan damtsin uwa, Allah wadai

    ReplyDelete
  2. Irinsu ke jawo mana balai a cikin al'umma

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN