Ka yi amfani da salon da aka gano matar da ta zage ka a wayar salula a 2019 don ceto daliban FGC Birnin Yauri - Kalubale ga Bagudu

Ka yi amfani da salon da aka gano matar da ta zage ka a wayar salula a 2019 don ceto daliban FGC Birnin Yauri - Kalubale ga Bagudu


An roki Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya yi wa Allah ya yi yunkuri na karshe domin ceto daliban kwalejin FGC Birnin Yauri da ke hannu Yan ta'adda kafin babban zaben 2023. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Malam Yusu (Ba ainihin sunan ba saboda dalilan tsaro), dan uwa ga daya daga cikin mahaifin dalibai da ke hannun yan ta'addan ya bukaci Gwamna Bagudu ya yi amfani da salon da jami'an tsaron jihar Kebbi sukayi wajen ganowa tare da kama matar da ake zargin ta zage shi a wayar salula a garin Yauri a 2019 domin ganowa tare da kubutar da daliban FGC Birnin Yauri da ke hannun Dan bindigan daji Dogo Gide. 

A ranar 10 ga watan Janairu 2023 Jaridar Aminiya ta wallafa Labarin cewa dan bindiga Dogo Gida ya bukaci a biya N100m kafin ya sako daliban.

Kazalika a can baya jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Dogo Gide ya auri daya daga cikin Yan matan da sace kuma yana rike da su.

Kawo yanzu dai, shafin labarai na isyaku.com bai sami wani bayani ko martani a hukumance daga mahukuntan jihar Kebbi dangane da zargi da ke yawatawa a jaridu dangane da lamarin ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN