Gaskiya ta fito: Burtaniya ta gayyaci Atiku don wata ganawar sirri, an gano abin da suka zanta akai

Gaskiya ta fito: Burtaniya ta gayyaci Atiku don wata ganawar sirri, an gano abin da suka zanta akai


Majalisar kamfen din takarar shugaban kasa ta jam'iyyar PDP ta bayyana dalilin da yasa gwamnatin kasar Burtaniya ta gayyaci Atiku don tattaunawa dashi, New Telegraph ta ruwaito. Legit.ng ta wallafa.

A cewar majalisar, an gayyaci Atiku ne domin tattauna batutuwan da suka shafi gamayya da hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Burtaniya a nan gaba idan ya gaji Buhari.

Wannan na fitowa ne daga daraktan yada labaran majalisar, Otunba Dele Momodu a cikin wani sako da ya bayar a jiya Talata 10 ga watan Janairu.

Momodu ya kuma bayyana cewa, akwai haske mai kyau game da nasarar Atiku a zaben da za a gudanar a cikin watan Fabrairu mai zuwa, rahoton Vanguard.

A cewar sakon nasa:

"Majiya ciki ta naqalto cewa, zaben ciki gida a na gwamnatin Burtaniya ya nuna AA (Atiku Abubakar) ne dan takarar da kan gaba kuma akwai yiwuwar aiki kafada-kafada dashi don amfanin kasashen biyu.

"Wannan na da matukar muhimmanci domin Burtaniya na son habakawa da fadada alakar kasuwanci da Najeriya."

Rikicin da ke gaban Atiku a matakin jam'iyya

Duk da wannan, har yanzu dan takarar na shugaban kasa a PDP na ci gaba da fuskantar barazana da koma baya a jam'iyyar, kasancewar akwai wasu jiga-jigan jam'iyyar da ke adawa dashi.

Gamayyar gwamnonin G-5 na ci gaba da nuna adawa da shugabancin PDP a matakin kasa, kana sun ce babu ruwansu da Atiku.

Gwamnonin dai burinsu shine; su ga an tsige Ayu Iyorchia ammatsayin shugaban jam'iyyar na kasa tare da ba wani dan yankin Kudu.

Burtaniya ba za ta tsoma baki a zaben bana ba

Wannan na fitowa ne daga bakin Ms Catriona Laing, babbar kwamishiniyar Burtaniya a Najeriya lokacin da take magana game da zaben na bana.

Ta kuma bayyana cewa, kasar ta Turai za ta tsaya ne tsaka-tsaki kan dukkan abubuwan da za su faru a zaben.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN