Duba Sanata da bai taba rike sabbin kudi da aka canja ba, duba dalili


Nan da ‘yan kwanaki za a daina amfani da tsofaffin takardun N200, N500 da N1000 a Najeriya, amma ana yawan kukan karancin sababbin kudi. Legit.ng ya wallafa.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa daga cikin masu kukan har da Muhammad Ali Ndume, wanda ya ce har yanzu bai ci karo da sababbin takardun ba.

Duk da yana cikin manyan ‘yan majalisar dattawan kasar nan, Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce bai rike sabuwar N1000 da sauran kudin da aka buga ba.

‘Dan siyasar yake cewa idan aka tafi a haka, mafi yawan ‘yan Najeriya za su gamu da cikas a dalilin matakin nan da babban bankin kasar nan ya dauka.

Dan majalisar Kudancin jihar Bornon ya shaidawa Vanguard haka, sannan ya kara da sukar mutanen da ke siyasantar da canjin kudin da CBN ya yi.

Sanatan yake cewa ba a kowane tsari ko manufa da aka fito da shi za a rika biyewa siyasa ba.

Da aka tambayi Ndume ra’ayinsa a game da wa’adin da aka bada na 31 na Junairun 2023, sai ya nuna cewa bai tunanin lokacin da aka kayyade zai isa.

“Lokacin ba zai yiwu ba, shiyasa na kawo magana a zauren majalisar dattawa, mu na rokon CBN ya tsawauta wa’adin domin a iya karbar tsofaffin kudi.

Yanzu mu na jiran CBN ne ya bada sanarwar tsawaita wa’adin, amma har yanzu ba su yi. Abin takaicin shi ne har zuwa yanzu babu sababbin kudin nan.

- Mohammed Ali Ndume

Kamar yadda Ndume yake fada, su na so ne a kara tsawon wa’adin zuwa karshen watan Yuni.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN