Duba jerin Jami'o'in Tarayyar Najeriya da suka kara kudin makaranta


Bayan gazawar kungiyar da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta yi na matsawa gwamnatin tarayya ta karo kudin kula da jami'o'i, wasu fittatun jami'o'in gwamnati a Najeriya sun kara kudin makaranta. Legit.ng ta wallafa.

Da dama cikin jami'o'in kasar sun sanar da karin kudi fiye da kashi 200 cikin dari wurin rajista da kudin makaranta a cewar rahoton The Punch.

Ga jerin wasu daga cikin jami'oin tarayyar da suka yi karin kudin makaranta.

Gwamnatin Tarayya ta Dutse

Gwamnatin tarayya ta Dutse, kamar yadda rahotanni suka zo ta yi karin kudin makaranta na zangon karatu na shekarar 2022/2023 cikin takardar da ta fitar a Disamban 2022.

Domin saukakawa iyayen yara biyan kudin, jami'ar ta bada daman yin biya biyu, kashi 60 a zangon karatun farko sai sauran kashi 40 a zango na biyu.

Jami'ar Maiduguri (UNIMAID)

Jami'ar Maiduguri ta ce ta yi karin kudin makarantar ne saboda hauhawar farashin kaya a kasar. Ga jerin wasu kudaden da ta yi karin.

Gwamnatin Tarayya, Lafia (FuLafia)

Jami'ar Tarayya ta Lafia, Jihar Nasarawa, ita ma an rahoto ta yi karin kudin makaranta ya kai N150,000 ga wasu tsangayan karatun.

Daga cikin su akwai daliban likitanci da za su biya N150,000

Amma, ba a musu karin kudin rajista.

Jami'ar Uyo (UniUyo)

Tsaffin dalibai na Jami'ar Uyo a baya suna biyan N50,000. Amma, yanzu an yi karin kudin zuwa N100,000.

Daga cikinsu, akwai daliban likitanci da za su rika biyan N105,750 yayin tsaffin dalibai za su biya N107,750.

Tsaffin dalibai na tsangayar ilimi za su biya N75,750 yayin da tsaffin dalibai za su biya N77,750.

Jami'ar Noma Ta Micheal Okpara, Umudike

Jami'ar Noma ta Micheal Okpara, Umudike ita ma ta yi karin kudin makaranta, sun ce kudin ayyuka sun karu.

Jami'ar ta sanar da hakan ne a Disamban 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN