DPO na yan sandan Najeriya ya yanke jiki ya fadi ya mutu a cikin ofis

DPO na yan sandan Najeriya ya yanke jiki ya fadi ya mutu a cikin ofis 


DPO na sashen ‘yan sanda na Seme a jihar Legas, SP Mojeed Salami,  ya mutu a ofishinsa a ranar Talata, 10 ga watan Janairu.

Majiyoyin ‘yan sanda sun ce marigayin ya koka da ciwon kai a ranar kuma ya ziyarci asibiti.  Ya dawo amma har yanzu ba shi da lafiya.  Ya gaya wa odalinsa ya kira masa DCO ya zo ofishinsa, amma lokacin da odali na dawo ya tarar da DPO kwance a kasa yana neman shaka iska da kyar.  An garzaya da shi babban asibitin Badagry inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce.

 “Ya rasu ranar Talata.  Abin ya ba kowa mamaki domin babu wani abu mai tsanani game da lafiyarsa.  Sun ce kawai ya koka da wani karamin ciwon kai, ya je asibiti, ya dawo, ya fara aiki kuma ya mutu ba da jimawa ba.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN