Da duminsa: An yi wa dan Luwadi daurin shekara 10 a gidan Yari, duba daliliA ranar Alhamis ne wata kotun yankin Zuba ta yankewa wani dan kasuwa mai suna Masiru Sadiq mai shekaru 37 hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari bisa samunsa da laifin yin luwadi da wani yaro dan shekara tara.

Sadiq na Kamkara Zuba, Abuja an yanke masa hukunc bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa.

Ya roki kotun da ta yafe masa kuma ta yi masa adalci da jin kai.

Alkalin kotun, Mista Mohammed Sani ya ce wanda aka yanke wa hukunci ba shi ne laifi na farko ba kuma ya ki ba shi zabin tara.

Sani ya kuma umarci wanda aka yankewa hukuncin da ya biya N50,000 a matsayin tarar kotu bayan ya kammala zaman gidan yari ko kuma ya yi zaman gidan yari na shekaru biyu a madadin tarar.

Ya ce hukuncin zai zama izna ga wasu kuma ya gargadi wanda aka yanke masa hukuncin zama dan kasa nagari kuma mai kyakykyawan hali kuma ya daina aikata laifi bayan ya kammala zaman gidan yari.

Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, Chinedu Ogada ya shaida wa kotun cewa a ranar Jan.  7 da misalin karfe 9: na dare wata kungiyar 'yan banga a Zuba ta kama tare da kawo mai laifin zuwa ofishin 'yan sanda na Zuba.

Ogada ya ce a ranar ne wani yaro dan shekara 9 ya kai rahoton lamarin ga kungiyar ‘yan banga na al’umma.

Ogada ya shaida wa kotun cewa a lokacin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike da kuma yi musu tambayoyi wanda ake tuhumar ya amince da aikata laifin.

Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 284 na kundin laifuffuka.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN