Da dumi-dumi: Majalisar Masarautar Zazzau ta kori wani Digarin Sarki bisa zargin yi wa wata Amarya fyade

Da dumi-dumi: Majalisar Masarautar Zazzau ta kori wani Digarin Sarki bisa zargin yi wa wata Amarya fyade


Majalisar Masarautar Zazzau a jihar Kaduna ta kori wani Dogari bisa zargin laifin yi wa wata mata fyade tare da gungun wasu mutane. Shafin isyaku.com ya samo.

Abdullahi Aliyu Kwarbai, Jami’in Yada Labarai na Sarkin, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 11 ga watan Junairu, 2023, ya ce, “An kori Sama’ila Abubakar Rimin Tsiwa, Dogari, ba tare da bata lokaci ba daga aikin fadar Majalisar Masarautar Zazzau sakamakon yi wa wata mata fyade a kan wata manufa,"

Matar da ke shirin bikin aurenta, an ce ta nemi taimakon Sarkin ne ta hannun Dogarin.

Maimakon wanda ake zargin ya kai matar wurin Sarki, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, sai ya kai ta wani wuri tare da abokansa inda suka yi mata fyade.

"Wata mace da ke shirin bikin aurenta tana neman taimako daga Sarki ta je wurinsa (Sama'ila), domin a kai ta gaban Sarki amma maimakon ya yi haka, sai ya yaudare ta zuwa wani wuri tare da abokansa, aka yi mata fyade."  sanarwar ta karanta.

"Majalisar ta umurci 'yan sanda da su gaggauta gudanar da bincike tare da tabbatar da gurfanar da masu laifin ba tare da bata lokaci ba."

Sanarwar ta bayyana cewa, majalisar Masarautar ta yi alkawarin bin diddigin lamarin don ganin an yi adalci ga wanda abin ya shafa.

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN