Kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar Osun da ke zamanta a Osogbo ta soke zaben Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP. NAN ya wallafa.
Shugaban kwamitin mutane uku, Mai shari'a Tertsea Kume, ya ce zaben gwamnan da aka yi a ranar 16 ga Yuli, 2022 bai bi dokar zabe ba.
Tertsea ya ce hakika an yi zaben da ya wuce adadi a kananan hukumomi shida na jihar.
Daga ISYAKU.COM
Rubuta ra ayin ka