Da dumi-dumi: An kama safeton yan sanda da ke yi wa dilolin miyagun kwayoyi safarar buhuhunan tabar wiwi

Da dumi-dumi: An kama safeton yan sanda da ke yi wa dilolin miyagun kwayoyi safarar buhuhunan tabar wiwi


Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, sun bankado wasu tarin tabar wiwi a dazuzzukan Opuje da ke jihar Edo, inda aka lalata wasu manya-manyan shaguna da tantuna da ake ajiye sama da kilogiram 317,417 (317.4 metric tons) na sinadarin da aka lalata tare da kona su a wani aiki na kwana biyu da hukumar ta yi.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya fitar, ya ce wani da ake zargi Omoruan Theophilus, mai shekaru 37, wanda ya yi ikirari a matsayin sifeton 'yan sanda, ya shirya domin kai tabar wiwin daga dazuzzuka zuwa birane da wasu mutane uku da aka bayyana sunansa da Aigberuan Jacob mai shekaru 42;  An kama Ekeinde Anthony Zaza mai shekaru 53 da kuma Naomi Patience Ohiewere mai shekaru 42 a kan zargin da ake yi da miyagun kwayoyi.

Hakazalika, hukumar a ranar Alhamis 19 ga watan Janairu ta yi aiki kan bayanan sirri da ta samu daga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar Amurka ta kama wasu masu aikata laifuka da ke da hannu wajen safarar kudaden dalar Amurka ta bogi a Legas.

A wani samame da jami’an NDLEA suka kai tare da abokan aikinsu na EFCC, an gano jimillar dalar Amurka 269,000 na jabun dalar Amurka a unguwar Oniru Shoprite da ke Lekki, Legas, inda aka kama wasu mutane uku da ake zargi. 

Latsa nan ka karanta sabbin labaran Duniya 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN