An karya lagon tsageru: An yi bata kashi da 'yan bindiga, an hallaka tsageru 4 nan take


Rundunar Operation Forest Sanity ta hallaka wasu ‘yan ta’adda hudu tare da kwato makamai da wasu kayayyakin aikata kaifi a jihar Kaduna. Legit.ng ta wallafa.

Wannan na fitowa ne daga bakin Manjo Janar Musa Danmadami, daraktan yada labarai na gidan soja a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja.

Danmadami ya bayyana cewa, jami’an tsaron sun kuma dakile harin ‘yan bindiga a yankin Rafin Sarki a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a ranakun Lahadi da Litinin.

Ya kuma kara da cewa, an fatattakin ‘yan bindiga tare da kashe biyu da kuma kwato makami AK-47.

Ya kada da cewa, rundunar a ranar Talata ta yi kwanton bauna ga ‘yan bindiga kan wasu ‘yan bindiga a kauyen Rafin Taba, inda aka kashe ‘yan ta’adda biyu.

Ya ce jami’ai sun kwato bindigogi AK-47, alburusai, wayoyin hannu, adda, babura guda biyu da kudi N206,000.

Sanarwar ta ce:

"Babban ofishin rundunar sojoji ta yabawa dakarun Operation Forest Sanity kuma tana karfafawa jama'a gwiwa da su ba sojoji sahihan bayanan ‘yan ta’adda masu aikata laifuka.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN