Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke tsakanin garuruwa biyu a Najeriya, an rasa rayuka


Mutane biyu sun rasa rayukansu a ƙauyen Koresu, yankin manoma a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo lokacin da wasu ɗauke da bindigu suka kai harin ɗaukar fansa. Legit.ng ta wallafa.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa waÉ—anda aka kashe sun haÉ—a da Kansila mai wakiltar yankin da kuma wani ÆŠan Banga da aka gano sunansa Kayode.

Har yanzun ba'a gano ainihin sunan Kansilan ba. An tattaro cewa yan bindigan sun kai harin ne ranar Asabar sakamakon harbe wata mata a kauyen Kajola, ƙaramar hukumar Okotipupa.

'Yan bindigan waɗanda ake zargin matasan Ikale ne sun yi kaca-kaca da gonakin mutanen ƙauyen. Wani mai suna Christiana Umukoro, ya tabbatar da harin yace mahaifinsa ya ci duka a hannun maharan.

Ya bayyana cewa kusan kashi 95 cikin 100 na mazauna ƙauyen sun tsere domin ceton rayuwarsu.

Mashawarci na musamman ga gwamna Oluwarotimi Akeredolu kan harkokin tsaro kuma kwamandan Dakarun Amotekun, Chief Adetunji Adeleye, yace tuni aka kai gawarwakin mutanen biyu É—akin ajiyar gawa.

Wane mataki hukumomi suka É—auka?

Adeleye, wanda ya musanta kashe dakarun Amotekun a harin, yace komai ya koma dai-dai a ƙauyen. Yace an jigbe sojoji, yan sanda da jami'an Amotekun a ƙauyen.

A cewarsa, "Akwai wata tsohuwar gaba tsakanin iyalan Oluku na Ikale a Okotipupa da manoman Oyo/Osun dake zaune a ƙaramar hukumar Odigbo."

"Mutanen Oyo/Osun manoma hatsi ne kuma suna faÉ—a da juna ne kan mallakin gonaki. Wannan sabuwar rigimar ta kunno ne bayan an harbi wata mata 'yar Kajola."

"Muna zargin matasan Ikale suka kai harin É—aukar fansa kan manoman, an kashe Kansilan yankin Oyo/Osun kana an kashe ÆŠan Banga É—aya ba wai É—an Amotekun ba."

Jami'ar hulÉ—a da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar Osun, SP Funmilayo Odunlami, tace babu É—an sandan da harin ya shafa kuma nan ba da jimawa ba hukumar zata fitar da bayanai.

Wasu daga cikin yan ta'addan ƙungiyar Boko Haram da suka zubar da makamansi sun bayyana wasu abubuwa da suka shafi tsohon shugabansu, Abubakar Shekau.

A cewarsi tubabbun yan ta'addan, Shekau ya mutu ya bar kwarkwara sama da 80. Idan baku manta ba kungiyar ISWAP ce ta yi ajalin Shekau.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN