Akalla mutane 55 da suka hada da matan mayakan Boko Haram da kuma kungiyar da ke adawa da su, ISWAP, aka kashe a wani fada da aka shafe mako guda ana yi a jihar Borno, kamar yadda majiyoyi suka bayyana. Legit ta wallafa.
Daily trust ta ruwaito cewa rikicin ya fara ne a makon da ya gabata a daya daga cikin sansanonin da ke yankin Mutakinti a karamar hukumar Bama a jihar, inda kimanin mayakan Boko Haram 11 da ke biyayya ga (JAS) suka rasa rayukansu a arangamar.
Abin da ya kai ga harin na baya-bayan nan na kungiyoyin biyu
Wata majiya mai tushe wacce ke da masaniya a kan lamarin, ta shaida wa jaridar cewa wani fadan da aka yi a yankin dala a dazuzzukan Sambisa a ranar Asabar din da ta gabata ya kuma yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da suka hada da mayaka da mata.
Majiyar ta kara da cewa mayakan na ISWAP sun fi karfin JAS kuma mayakan 11 sun mutu a wani artabu da aka yi a yankin Mantari.
Vanguard ta rahoto cewa rikicin ya faru ne a yankin Dollar Land, Mantari, Mutakinti general area duk a karamar hukumar Bama da kuma Bayan Dushai a karamar hukumar Gwoza.
Yayin da yake tabbatar da lamarin, Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, ya yi ikirarin cewa mayakan da ke Sambisa sun so daukar fansa ne kan kashe Kwamandansu, Malam Aboubakar (Munzir) da wasu mayakan 15 da aka kashe a wani kazamin fada da aka yi.
Boko Haram sun rama
Mayakan Boko Haram sun kashe akalla mata 33 na 'yan ta'addar Daesh a yankin yammacin Afirka (ISWAP) a jihar Borno.
Wani kwararre a fagen yaki da ‘yan tada kayar baya, Zagazo Makama, ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 5 ga watan Disamba.
Makama ya ce,
“Daga baya kungiyar ISWAP ta ja da baya inda suka dauki matsayi a sansanin Izzah. Daga nan ne suka koma Garin Abbah mai tazarar kilomita 2 inda suka dunkule domin jiran 'yan Boko Haram.
“Amma maimakon su gana da ‘yan kungiyar ta ISWAP domin ci gaba da yakin, ‘yan Boko-Haram sun zagaya inda suka nufi inda matan ISWAP suke inda suka kashe 33 daga cikinsu.
"A kwanaki masu zuwa za a ga yadda mayakan ISWAP za su mayar da martani game da kisan gilla da 'yan Boko Haram suka yi wa matansu."