Kwamishinan ya yi bayanin hakan ga manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Gwadangaji, da kuma sanarwar manema labarai da ya fito daga ofishinsa ranar Talata.
Sanarwar ta ce:
"A ranar 2 ga Disamba, 2022 da misalin karfe 7pm, wata Zara'u Sahabi 'f' 'yar shekara 25 a kauyen Kwaku, gundumar Kaoje, a karamar hukumar Bagudo, a dakinta, ta yi amfani da itace ta buga wani Gadafi Nasiru 'm' mai shekaru 3 a duniya.a kai. Sakamakon haka, ya mutu nan take.
Bayan samun rahoton, tawagar ‘yan sanda ta garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka cafke wanda ake zargin.
A yayin gudanar da bincike, ta amsa laifin ta. Za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike."