Yan bindiga sun yi wa wata mata mai ciki fyade har ta mutu a jihar arewa


Wasu ‘yan ta’adda sun yi wa wata mata mai ciki, uwar ‘ya’ya uku fyade har lahira a kauyen Dnakundna da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a lokacin da matar ta je tserewa harin ‘yan bindigar amma sai ta fada hannun wasu daga cikin yan bindigan.

Majiyoyi daga al’ummar yankin sun shaida wa jaridar The Nation cewa, ‘yan ta’addan sun dora wa mutanen kauyen harajin Naira miliyan 2 don ba su damar girbi a gonakinsu.

Amma an tattaro cewa mutanen kauyen sun kasa biyan kudin, wanda hakan ya fusata ‘yan fashin.

Don gudun kada a kai musu hari, mutanen kauyen, musamman mata da yara a yawansu, sun yanke shawarar barin kauyen amma ba su san cewa an riga an sanar da ‘yan fashin gudun hijirar da suka yi ba, kuma suka yanke shawarar yin kwanton bauna.

Matar mai ciki ba ta yi sa'a ba yayin da ita da 'ya'yanta uku suka shiga cikin kwanton baunar, kuma aka tasa keyarsu zuwa cikin daji.

Bayan sun yi mata fyaden da bai wuce bakwai ba, an bar mata da raunuka a jikin ta.

Iyalinta ne suka kai ta asibiti amma ta rasu a daren Juma’a, 23 ga Disamba, 2022.

An tattaro cewa an yi awon gaba da mutanen kauyen da dama yayin harin.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN