‘Yan bindiga sun sace wani basarake bayan sun karya kofofar gidansa


Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Oloso na Oso a karamar hukumar Akoko North-West ta jihar Ondo, Oba Clement Jimoh Olukotun. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

An sace Sarkin Ondo daga fadarsa da misalin karfe 10:15 na dare a ranar Alhamis 1 ga watan Disamba.

Majiyoyi sun shaida wa jaridar The Nation cewa ‘yan bindigar sun yi harbi ne a kofar gidan Oba bayan mutanen da ke cikin gidan suka ki bude kofar.  Babu wanda ya jikkata yayin harin.

Wata majiya ta ce;

“Lokacin da suka zo, sai suka kewaye ginin, suka fara umurtar sarki da sauran mutanen da ke cikin gidan da su bude kofar su mika wuya, amma babu wanda ya amsa.

"A nan ne suka fara harbi, suka lalata babbar kofar suka shiga, suka yi wa Kabiyesi da 'yan uwansa barazana kafin suka fitar da shi suka tafi da shi, ba a tuntubi ko daya daga cikin dangin ba amma mun san cewa masu garkuwa da mutane ne."

Kakakin rundunar ‘yan sandan Ondo, Funmilayo Odunlami, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce;

“Gaskiya ne amma har yanzu ba a san cikakken bayanin abin da ya faru ba, amma an tura ‘yan sanda daga hedkwatar ‘yan sanda reshen Oke-Agbe hedikwatar karamar hukumar Akoko Northwest a jihar Ondo domin gudanar da bincike a garin”.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN