Yan bindiga sun yi wa Sarki a Zamfara kwanton bauna suka kashe shi
Wasu ‘yan bindiga sun kashe Hakimin Yankuzo, Alhaji Hamza Abdullahi Kogo na Masarautar Tsafe a jihar Zamfara.
Majiyoyi sun shaida wa gidan Talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun kai wa hakimin hari a kan hanyarsa ta komawa al’ummarsa daga wata ganawar hukuma da aka yi ranar Juma’ar da ta gabata 9 ga watan Disamba da misalin karfe 8 na dare.
An harbe shi tare da raunata shi a yunkurin sace shi. An garzaya da Kogo zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Gusau, babban birnin jihar inda daga bisani ya rasu a daren Asabar.