"'Yan bindiga ne mayakanmu": Kalamansa sun jawo bacin rai yayin da Sheikh Gumi ke gaya wa 'yan Arewa wadanda za su zaba
Babban Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya gargadi ‘yan Arewa kan zaben ‘yan siyasar da ba za su yi sulhu da ‘yan bindiga da ke haddasa rikici a yankin ba. Legit.ng ta ruwaito.
A yayin daya daga cikin hudubobinsa na baya-bayan nan, Gumi ya bayyana ‘yan bindiga a matsayin mayaka wadanda bai kamata a kashe su ba amma an yi shawarwari da su, in ji rahoton PM News.
“Kada ku zabi wadanda za su yaki ‘yan bindiga. Mayakan su ne mayakanmu a dajin...... Mutanen mu a cikin dajin.
"Don haka ku zabi wadanda bayan sun sami mulki za su yi kira da tattaunawa da mutanenmu ('yan bindiga) don ba su abin da suke so don zaman lafiya ya yi mulki."