Yadda ta kwabe wa wasu matasa da yan mata da suka halarci daurin auren yan Luwadi a Kano

Hukumar Hisbah ta Kano ta kama wasu matasa da suka halarci daurin auren luwadiHukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa 19 da suka halarci daurin auren jinsi daya.

Kakakin Hisbah, Malam Lawan Ibrahim, ya ce matasan sun taru ne domin shaida daurin auren wasu da ake zargin 'yan luwadi ne, Abba da Mujahid.

Ibrahim ya kuma ce wadanda aka kama za a mika su ga ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace.  Yace;

“An kama shi ne bayan da wani Basamariye nagari ya rada wa hukumar game da auren Yan luwadin.

“Jami’an mu da ke hedikwatar hukumar Hisbah, Sharada Kano, sun isa wurin kafin a fara daurin auren.

“A cikin wadanda aka kama akwai mata 15 da maza hudu.

“Abba da Mujahid sun tsere nan take jami’an Hisbah suka isa wurin daurin auren, amma mai shirya bikin, Salma Usman, ‘yar shekara 21, tana hannunmu.

“Wadanda aka kama za a mika su ga ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace kamar yadda akasarin matan suka ce an gayyace su zuwa daurin auren ne daga jihohin makwabta.

"Za mu kara kaimi wajen ganin an kama Abba da Mujahid."

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN