Yadda Sanatan PDP ke yi wa Tinubu yakin neman zabe, ya fadi dalili


Sanata Chimaroke Nnamani na Jam’iyyar PDP, ya bukaci matasan Najeriya su zabi dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu a zaben 2023. Rahotun Jaridar Aminiya ta wallafa.

Sanata Nnamani ya ce hikimar matasa su zabi Tinubu shi ne dan takarar na da kyawawan manufofi na kyautata rayuwarsu, kuma zai tafi tare da su.

Nnamani ya ce, tun a lokacin Tinubu ke Gwamnan Jihar Legas a 1999 ya fahimci “barin matasa kara zube matsala ce, don haka ya kawo tsare-tsaren farfado da tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga akasarin mutanen jihar, wadanda galibi matasa ne.”

Tsohon Gwamnan na Jihar Inugu daga 1999 zuwa 2007 ya bayyana cewa Tinubu tsare-tsare maso dorewa da Tinubu ya bullo da su sun taimaka wajen magance matsalar zaman banza, duk kuwa yawan matasa da ke tururuwar zuwa jihar don neman abin yi.

A cewarsa, a lokacin, dan takarar ya kuma bullo da shirin wayar da kan matasa kan illar da ta’ammali da miyagun kwayoyi ke wa rayuwar matasa.

“Sannan ya ba wa kowace kungiyar matasan da suka yi rajista don kashin kansu tallafin Naira miliyan daya domin ci gaba da aikin wayar da kan matasa su zama masu amfanar al’umma.

“Ya kuma kara kudaden hukumomin gudanar da shirin sannan ya gina cibiyar sauya dabi’un masu shan kwayoyi ta yadda za su iya zuwa makaranta da kuma koyon sana’a domin dawo da kimarsu, a  cikin yanayi mai inganci.

“A 2003 cibiyoyin koyon sana’a da sauya dabi’un ’yan daba da masu kwana a kan titi suka fara aiki inda aka kara karfafa su ta hanyar koyar da sana’o’in hannu domin dogaro da kai”, in ji Sanata Nnamani.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN