Yadda bom ya kashe karamin yaro a jihar arewa

 Yadda bom ya kashe karamin yaro a Borno


Bom ya tarwatsa wani karamin yaro, tare da jikkata wasu abokansa a garin Banki da ke Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno. Rahotun Jaridar Aminiya.

Yaron mai shekara 14 ya gamu da ajalinsa ne bayan shi da wasu abokansa biyu sun dauki bam din a cikin rashin sani, a yayin da suke neman tarkacen karafa a wajen garin na Banki a ranar Laraba.

Shaidu sun ce da farko ya yi kokarin ya fasa shi da wani karfe, yana zaton karfe ne na jari-bola, amma ya kasa fasawa.

Sun shaida wa Zagazola Makama, wani mai sharhi kan tsaro kuma kwararre kan yaki da tada kayar baya a Tabkin Chadi, cewa bayan yaron ya kasa fasa bom din ne ya dauka ya je gida da shi.

Zuwansa gida ke da wuya, sai ya nufi inda mahaifiyarsa take girki ya sanya shi a wuta da nufin ya narkar da shi.

Nan take bom din ya tashi, ya yi gunduwa-gunduwa da yaron tare da ji wa abokan nasa biyu munanan raunuka.

Lamarin dai ya haifar da damuwa a tsakanin al’ummar yankin, musamman a yanzu da gwamnatin jihar ke mayar da dubban ’yan gudun hijira zuwa garuruwansu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN