Wani dan Kaduna ya kai kawar matarsa kara Kotu bisa zargin satar awakinsa guda 4


Wani manomi, Adnan Sani, a ranar Alhamis, 22 ga watan Disamba, ya kai Saudat Bagobiri, kawar matarsa ​​a gaban kotun shari’a da ke zamanta a Kaduna bisa zargin sace masa awaki guda hudu.

Wanda ya shigar da karar ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ta taba mayar da guda biyu daga cikin akuyoyinsa da suka bace, ta kuma bukaci ya ara mata talotalo namiji don ta hada shi da talotalonta mace don ya yi barbara.

"WaÉ—annan awaki biyu da ta dawo da su sun sake bacewa, sai muka tarar da wata akuya tawa a daure a gidanta.

“Ta mayar da talotalon din namiji amma ina zarginta da sace awakina guda hudu, sai ta yaudari matata ta dauka cewa kawarta ce, kawai ta kusance matata don ta sace mana dabbobin mu.” Inji shi.

A nata bangaren, wadda ake kara ta ce ba ta san komai ba game da bacewar awaki.

"Na iske akuya daya yana yawo a harabar gidana saboda nima ina kiwon akuya, da na samu akuyar sai na kira shi domin ya duba ko akuyar nasa ce, sai ya tabbatar da cewa lallai nasa ne, ya dauki akuyar ya tafi," in ji ta.  .

Alkalin kotun, Salisu Abubakar-Tureta, ya yi watsi da karar yana mai cewa duk ikirarin da mai karar ya yi zato ne kawai.

Alkalin ya sallami wanda ake tuhuma.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN