Tashin hankali yayin da aka gano masana'antar hada bama-bamai mafi girma a jihar kudu-maso-gabas a Najeriya


Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, ta ce ta gano babbar masana’antar bama-bamai a yankin Kudu maso Gabas.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, Chris Anyanwu ya bayyana cewa, an gano masana’antar da ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da reshensu masu dauke da makamai, wato Eastern Security Network (ESN) ke gudanar da ita bayan da aka samu labarin ayyukan ‘yan kungiyar.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Anyanwu ya tabbatar da cewa ‘yan sanda sun samu sahihin bayanai kan ayyukan ‘yan ta’addan a Obegu da ke kan iyaka tsakanin Onicha-Isu da karamar hukumar Ishielu ta jihar Ebonyi.

Anyanwu a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce ‘yan kungiyar da aka haramtawa ‘yan sandan sun yi artabu da jami’an ‘yan sanda a wata musayar wuta inda suka kashe ‘yan kungiyar IPOB/ESN guda biyu tare da cafke wasu kwamandojin su.

 Kalamansa:

“An yi gaggawar tafiya tare da tawagar jami’an ‘yan sanda da ke aiki a sashin Ohaukwu ya kai ga kama Sunday Ubah aka Bongo, kwamandan IPOB/ESN na jihar Ebonyi.

“Babban wanda ya bayar da bayanan sirri game da ayyukan da kuma yadda ake tafiyar da masu laifin, tun da farko ya yi ikirarin cewa shi ne PRO kuma dan asalin Umunnochi a karamar hukumar Isuikwuato, jihar Abia.”

“Duk da haka, bincike da magabatansa suka yi tare da rundunar ‘yan sanda ya tabbatar da cewa shi dan asalin Obegu ne, karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi kuma kwamandan sashen na Obegu ne”.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN