Ta faru ta kare: Matasa sun yi wa shugaban APC tsirara bayan sun lakada mashi duka a Nasarawa


Matasa sun yi wani jigo a Jam’iyyar APC Reshen Jihar Nasarawa tsirara bayan sun lakada mishi duka a bainar jama’a.

Matasan da ake kyauatata zaton magoya bayan jam’iyyar ne sun yi wa Abubakar Abu Giza dirar mikiya ne a lokacin babban gangamin yakin neman zabe da jam’iyyar ta shirya a jihar. Jaridar Aminiya ta wallafa.

Shugaban Kwamitin Shawara na Jam’iyyu IPAC a Jihar Nasarawa, Cletus Ogah Doma, ya tabbatar da faruwar lamarin, bayan an yada bidiyon abin da ya faru da Giza a Lafia, hedikwatar jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan mummunan abin ya faru da Abubakar Giza ne a Fadar Sarkin Lafia a ranar Alhamis.

Mista Ogah Doma wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar ZP Reshen Jihar Nasarawa, ya ce babu dalilin yi wa dan siyasar tsirara a bainar jama’a, don haka ya kirayi matasan jihar da su nisanci dabanci.

Ya ce ya kamata a ce an wuce matakin irin wannan kidahumanci, sannan a matsayin matasa na kashin bayan kowace al’umma da hadin kanta, bai kamata ba su bari miyagun ’yan siyasa na amfani da su wajen aikata ba daidai ba.

Shugaban na IPAC, ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da ma Jam’yyiar APC reshen jihar da su fito su yi Allah wadai da duk wani nau’i na dabanci da miyagun halayya da yunkurin kawo rabuwar kan al’umma.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN