Na mijin fama: Manomi mai mata 12, 'ya'ya 102 da jikoki 568 ya magantu, yana tunanin tsarin iyali (Hotuna)

Na mijin fama: Manomi mai mata 12, 'ya'ya 102 da jikoki 568 ya magantu, yana tunanin tsarin iyali (Hotuna)


Wani mutum dan kasar Uganda yana da mata 12 da ‘ya’ya 102, Mzee Musa Hasahya, ya sha alwashin ba zai kara samun ‘ya’ya ba yayin da yake kokawa kan yadda yake fuskantar babbar iyalinsa. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Manomin mai shekaru 67 a duniya a yanzu ya shawarci matansa na haihuwa da su rika shan kwayan maganin hana haihuwa.

A cewar jaridar Daily Star ta Burtaniya, Hasahya, yana jin radadin tsadar rayuwa a Bugisa, na kasar Uganda, inda yake zaune tare da manyan iyalansa.

"Ba zan iya jurewa haihuwa ba saboda karancin kayan aiki. Kuma a kan haka na shawarci dukkan matana da suka kai shekarun haihuwa da su je su yi tsarin kayyade iyali. Ina kuma hana masu son auren mata sama da hudu kada su yi haka saboda  abubuwa ba su da kyau,” inji shi.


Ya kara da cewa, "Kudaden da nake samu ya ragu da raguwa a cikin shekaru saboda tsadar rayuwa da kuma iyalai na suna karuwa da girma.

Musa, wanda kuma yana da jikoki 568, yana zaune ne a wani katafaren gida mai daki 12.  Ya auri matarsa ​​ta farko Hanifa a shekarar 1971 yana dan shekara 16.

Ya ce duk da yake yana iya raba ‘ya’yansa da jikokinsa, bai san su duka da sunan ba.

Ya auri matarsa ​​ta farko Hanifa a shekarar 1971 yana da shekara 16 bayan ya bar makaranta, kuma ya zama uba a karon farko bayan shekara biyu ta haifi diya mace.

A matsayinsa na shugaban kauyen kuma dan kasuwa, ya ce ya yanke shawarar kara wa iyalinsa ne saboda yana da kudi da fili.


"Saboda na sami wani abu, na yanke shawarar fadada iyali ta hanyar auri mata da yawa," in ji shi.

"Na tabbatar da cewa an samar da fartanya domin kowannen su ya yi noman kasa da kuma samar da abincin da zai ciyar da iyali tun da kasa na da albarka."

Sai dai a yanzu yana neman gwamnati ta taimaka masa, yana mai cewa yana kokawa da tarbiyyar ‘ya’yansa baki daya.

Amma duk da yawan zuriyarsa, danginsa sun ce gabaÉ—aya suna cikin koshin lafiya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN