Wata kyakkyawar mace mai suna @ohemaarosepapabi, ta shiga yanar gizo don raba wani bidiyo mai dauke da hotunan yadda ta kasance a baya da kuma bayan ta shiga aikin soja. Legit.ng ta wallafa.
Da take raba hotunan, ta gaya wa mutane su lura da yadda jikinta ya canza bayan ta zama soja.
A farkon faifan shirin, ta yi kama da mace sosai tare da haskaka dukkan sassan jikinta da tufafinta. Bayan dakika kadan ba'a gane fuskarta ta saka kayan hafsa.
A tsaye kusa da wani jami'in soja, matar ta yi wani guntun tsaki. Ta fito kwata-kwata daban da hotunanta na baya.
Latsa kasa ka kalli bidiyo