Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi ya kaddamar da kwamiti mai matukar mihimmanci gabanin zaben 2023


Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, CP Ahmed Magaji Kontagora, ranar Laraba 9/12/2022, ya gayyaci shuwagabannin hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki kan zaben 2023 a Aberta guest inn Birnin kebbi, domin gudanar da wani taro, inda ya yaba da yadda za a tabbatar da gaskiya, sannan an tattauna lamurra kan kalubalen ga zabuka da kuma mafita masu karbuwa a zaben 2023. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Biyo bayan fara gangamin yakin neman zabe daga dukkan jam'iyyun siyasa, fagen siyasa na aiki a halin yanzu kuma yuwuwar karuwar rashin zaman lafiyar siyasa na iya karuwa a fadin jihar. 

CP Ahmed Magaji Kontagora ya kaddamar da kwamitin tuntuba tsakanin hukumomin tsaro kan harkokin tsaro a yayin taron, bisa ga umarnin babban sufeton ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba. 

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN