Kuma dai: "Dakaren Birnin gwari" kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyar APC, Tinubu, ya sake baro magana, ya ce..

Kuma dai: "Dakaren Birnin gwari" Kuma Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar APC, Tinubu ya sake baro magana, ya ce.. 


Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya fadi kadan daga hanyoyin da za a bi wajen kawar da zaman banza a Najeriya. Legit.ng ta wallafa.

A wani bidiyon da wani jigon APC mazaunin Legas, Joe Igbowe ya yada Facebook, Tinubu ya yi magana kan wata kalma 'AGBADOnomics'

A cikin bidiyon, Tinubu ya bayyana meye ma'anar wannan kalmar ta 'Agbabonomic', inda ya bayyana dalla-dalla yadda 'yan kasar waje ke amfani da masara wajen yin abubuwa da yawa.

A bidiyon, Tinubu ya ce:

"Ban san me suke kiran masara ba sai da na zo Amurka. Kuma daga masararmu ne.

"Wannan abun da muke amfani da shi saboda cutar Korona, ban san daga masara ake yinsa ba, masarar da muke nomawa a nan.

"Haba, wane irin adadi za mu iya nomawa? Za mu iya mamaye yankin Afrika ta Yamma. Ya kamata mu yi shi a gida. Ya kamata mu yi abubuwa da yawa a gida. Za mu samar da ayyuka."

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN