Babban kotun tarayya da ke zamanta a Kano, a ranar Alhamis, ta tabbatar da Mohammed Sani Abacha, a matsayin halastacen zababben dan takarar gwamna na PDP a jihar Kano. Legit.ng ta ruwaito.
A hukuncinsa, a yammacin ranar Alhami, Mai sharia A.M. Liman ya soke zaben cikin gida da jam'iyyar ta yi inda Sadik Aminu Wali ya yi nasara.
Kotun ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta cire sunan Wali ta maye da na Mohammed Sani Abacha, rahoton The Punch.
Kotun ta amsa dukkan bukatun da mai shigar da kara ya nema a masa.