Kisan wanda ake zargi da dauke babur a Badariya: Ma'aikatar Shari'a ta Kebbi ta gurfanar da mutane shida a gaban kotu


Ma’aikatar shari’a ta jihar Kebbi ta gurfanar da wasu mutane shida a gaban kuliya bisa zargin kashe wani matashi da ake zargi da satar babur a Badariya a ranar 19 ga watan Satumba. 

Ma’aikatar a karkashin jagorancin Darakta mai gabatar da kara, ta jagoranci wasu Lauyoyi biyu a karar da ta gurfanar da wasu mutane shida da ake tuhuma a gaban wata babbar kotun jihar Kebbi da ke zamanta a Gwadangaji, 8 ga Disamba, 2022.

A ranar Alhamis ne masu gabatar da kara suka rufe bangarensu da shaidu tara.

Laifukan da ake tuhumar wadanda ake zargin sun shafi kisan kai, hada baki, sata da shiga gida.

Lauyoyi uku ne ke kan kariya ga hudu daga cikin wadanda ake tuhuma, sai kuma Lauyan na daban na sauran biyun da ake tuhuma.

Tun da farko dai kotun ta zauna ne a ranar 6 ga watan Disamba amma an dage sauraron karar zuwa ranar Alhamis 8 ga wata.  Har ila yau, Alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar Litinin 12 ga Disamba, 2022, saboda ana sa ran masu kare wadanda ake tuhuma za su gabatar da wasu karin shaidu biyu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN