Hisbah ta rufe wuraren shan giya sama da 100 a birnin arewa mai tarihi

Hisbah ta rufe wuraren shan giya sama da 100 a birnin arewa mai tarihi


Wata kungiyar addinin Musulunci mai zaman kanta mai suna Hisbah, ta jagorance garkame wuraren shan giya sama da 100 a Karamar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna. 

Jaridar Aminiya ta ruwaito Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Gari, Garba Datti Babawo ne ya tabbatar da hakan, yayin gabatar da hsaidar kammala karbar horo ga ’yan kungiyar su 750 da ya gudana a hedkwatar Karamar Hukumar ta Sabon Gari.

Dan majalisar ya ce tun da Karamar Hukumar take ba ta taba samun sa’ida daga ayyukan badala ba sama da lokacin da aka kafa rundunar ta Hisbah.

Daga nan sai Babawo ya ja kunnen dakarun da su tabbatar suna bin dokokin dokoki yayin gudanar da ayyukansu.

Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar ta Sabon Gari, Injiniya Mohammed Usman, ya jaddada kudurin gwamnatinsa na kakkabe yankin daga ayyukan masha’a, ta yadda za a sami yanayin kasuwanci mai kyau tare da bunkasa zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Tun da farko sai da Kwamandan rundunar a yankin, Abubakar Auwal ya ce dakarun su 750 sun sami cikakken horo a harkar tsaro kan yadda za su gudanar da ayyukansu.

Kwamnadan ya kuma ce 500 daga cikin dakarun maza ne, yayin da 250 kuma mata ne, kuma za su sadaukar da kawunansu wajen hidimta wa al’umma.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN