Gwamnatin Buhari na kokarin dawo da harajin da Isa Pantami ya hana a kakaba wa yan Najeriya


Gwamnatin tarayya ta na duba yiwuwar lafta haraji a kan harkokin sadarwa bayan an dakatar da maganar, hakan zai jawo yin waya ya kara tsada. Legit.ng ta wallafa.

Wani rahoto da muka samu daga Punch a ranar Juma’a ya nuna gwamnatin tarayya ta sake bijiro da wannan batu domin a aiwatar da shi a shekarar 2023.

Wannan bayani na cikin wata takarda da aka gani da za a gayyaci mutane domin tattauna kudirin tattalin arzikin 2022 a zauren majalisar wakilan tarayya.

Kwamitin harkar tattalin arziki na majalisar tarayyar kasar ya fitar da wannan takarda.

Ta koma, ta leko...

An fahimci harajin sadarwar da aka dakatar a shekarar nan, yana iya komawa gaban ‘yan majalisar wakilan Najeriya a kokarin da ake yi na samun kudin shiga.

Kwamitin harkar kudin ya ce zai zauna da al’umma domin jin ra’ayinsu a kan kudirin tattalin arziki na shekarar 2022, kuma za a tabo maganar harajin.

Daga cikin abin da takardar kudirin take cewa shi ne Najeriya za ta rika karbar haraji daga kamfanonin sadarwa a karkashin sashe na 13 na wannan doka.

Shugaban kasa ne yake da ikon yanke kason harajin da za a karba a wajen kamfanonin.

Rahoton ya ce kudirin ya nuna babban dalilin hakan shi ne ya taimaka wajen kara kudin shiga da harajin da gwamnatin tarayya za ta rika samu a shekara.

Nawa za a rika karba?

A takardar, ba ayi bayanin adadin harajin da za a rika yankawa kamfanonin sadarwar da ke kasar ba. A karshe dai za a tashi da biliyoyin kudi a asusu.

A watan Yulin 2022 da aka bijiro da tsarin, an yi niyyar karbar harajin 5% kamar yadda yake a kudirin tattalin arziki tun 2010, amma ba a iya aiwatar da shi ba.

Kafin ranar 21 ga kowane wata ya kamata kamfanoni su biya harajin. Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami ne ya roki a hakura saboda farashin waya zai tashi.

Bashir Machina v Ahmad Lawan

Idan aka shiga siyasa, za a ji labari kwamitin yakin neman zaben Bashir Machina a APC, ya ce Dr. Ahmad Lawan yana cin amanar Bola Tinubu a takarar 2023.

Amma kakakin kwamitin takarar Tinubu, Festus Keyamo ya karyata zargin, ya ce Lawan ba zai taba yin watsi da ‘dan takaran APC saboda Atiku Abubakar ba

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN