Dubu ta cika: An kama wani mutum da ake zargi da damfarar ma’aikatan POS

Dubu ta cika: An kama wani mutum da ake zargi da damfarar ma’aikatan POS


Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas da ke Rapid Response Squad sun cafke wani matashi dan shekara 26 mai suna Emmanuel Okoroafor bisa zarginsa da damfarar ma’aikatan POS na Point-of-Sale a jihar.

A shafin ta na Facebook, RRS ta rubuta;

''Emmanuel Okorafor mai shekaru 26 an kama shi da yammacin jiya a Ojota.  An kama shi da laifin zamba na ATM.  Ya furta cewa ya fara ne makonni uku da suka wuce.

Okorafor ya damfari ma’aikatan POS wasu makudan kudade.  Yakan ba su adadi a cikin bakwai, wanda ma’aikacin zai shigar da shi a POS dinsa (N52,000:00).  Da zarar an mika masa na’urar ya shigar da lambarsa tq sirri, sai ya yi wayo ya goge sifili biyu (N5,200:00) kafin ya mayar wa masu aikin POS.

Da wannan ne ma’aikatan suka biya shi N52, 000:00 yayin da ake cire masa N5, 200:00 kacal marmaki N52.000.00.

A cikin ikirari nasa, ya sake yin irin wannan zamba a wuraren POS biyar a jiya a kusa da Ogudu GRA da Ojota kafin a kama shi da yamma.

Kamar yadda ya faru a jiya, ma’aikatan POS guda uku sun ce ya yi musu wannan dabara.  ATM dinsa ya yi daidai da wanda aka yi amfani da shi wajen zamba.

Wasu daga cikinsu sun ce sun tuhumi tare da korar da yawa daga cikin hadimansu da sace kudadensu.

Bincike ya nuna cewa an yi amfani da na’urar ATM ne wajen karbar makudan kudade daga Naira 52,000 zuwa N5500 a wuraren POS da dama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN