Da dumi-dumi: Yan bindiga sun farmaki garin Kyabu da kewaye a Masarautar Zuru sun tafka ta'asa

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun farmaki garin Kyabu da kewaye a Masarautar Zuru sun tafka ta'asaYan bindiga sun kutsa garin Kyabu sun tafka barna tare da sace babura guda tara kuma suka banka wa uku daga cikin baburan wuta a karamar hukumar Danko Wasagu da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi.

Wani ganau da ido kuma wanda lamarin ya faru a garin ya ce tun da misalin karfe 3:00pm na rana yan bindigan suka dira garin Kyabu, kuma suka farmaki jama'ar kauyuka da ke kewaye suka kuma sace iya abin da za su iya sacewa daga gidajen jama'a yayin da jama'a a garin Kyabu da kauyuka na kewaye suka gudu domin neman mafaka a garuruwan Maga, Ribah da sauransu. 

Majiyarmu ta ce yan bindigan sun shiga yankin ne tun karfe 3 na rana kuma suka dinga cin karen su ba babbaka har karfr 11 na dare.

Kazalika majiyar ta ce mako daya kafin farmakin na ranar Litinin 26 ga watan Disamba, Yan bindiga sun farmaki wasu garuruwa a karamar hukumar Danko Wasagu suka tafka barna tare da gargada wasu mutane 10 bayan sun kashe mutum 1. Sai dai bayanai sun ce 2 daga cikin wadanda aka kama sun kubuta.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa yanzu haka akwai amfanin gona mai dimbin yawa a yankin Kyabu da kauyukan kewaye da jama'a suka gudu suka bari, kuma ana zargin cewa dabbobi na cinye amfanin gonar tare da fargaban sacewa tare da lalata saura.

Wannan lamarin na zuwa ne kwanaki kadan lokacin da jam'iyyun siyasan jihar Kebbi da suka hada da APC da PDP suka gudanar da tarukan siyasa don neman jama'a a kudancin jihar Kebbi. A gefe daya kuma jama'a a Masarautar Zuru na fama da matsalar rashin tsaro tare da cin mutunci daga hannun Yan bindiga. 

Sai dai mun samo cewa a mako da ya gabata, jami'an sojin Najeriya sun taka rawar gani wajen dakile kaifin barnar Yan bindiga a garin Shengel da kewaye, bayan an yi zargin cewa Yan bindiga sun farmaki yankin tare da tafka ta'asa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN