Da dumi-dumi: Ɗan wasan damben Najeriya ya yanke jiki ya faɗi matacce ana tsaka da dambe


Wani dan wasan dambe a gasar wasanni na kasa da ake yi a halin yanzu a Asaba, babban birnin jihar Delta ya rasu, Daily Trust ta rahoto. 

Legit ta ruwaito dan damben, Chukwuemeka Igboanugo, wanda ke wakiltar Imo, ya rasu bayan ya sha kaye hannun Prince Gaby Amagor daga jihar Anambra a rukunin masu daukin kilogiram 86. 

An naushi Pascal a kunchinsa hakan yasa alkalin wasa ya tsayar da damben lokacin da ya gaza tashi. 

Wani jami'in damben, wanda ya nemi a sakayya sunansa ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa: 

"Nan take aka fitar da shi daga filin damben saboda bashi kulawa kafin a garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar ya rasu." 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN