Da dumi-dumi: Kotu ta hana DSS kama gwamnan CBN Emefiele


Rahoton da jaridar TheCable ta fitar ya bayyana cewa wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta ki amincewa da bukatar da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gabatar na kama Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN). Legit.ng ta wallafa.

Da yake kin amincewa da bukatar Ex parte - wanda mai nema ya shigar, Mai shari'a JT Tsoho, babban alkalin kotun, ya ce rundunar 'yan sandan sirrin ba ta bayar da wata kwakkwarar hujja da za ta tabbatar da ikirarin da ta yi na cewa Emefiele na da hannu wajen bayar da kudaden ta'addanci da kuma laifukan da suka saba wa tattalin arziki ba.

Jaridar TheCable ta ruwaito wata majiya a babban kotun ta na cewa alkalin ya ce da a ba shi amana idan har akwai wata shaida da ke tabbatar da zargin.

“Alkalin ya kuma yi mamakin dalilin da ya sa aka sanya sunan wanda ake kara a matsayin ‘Godwin Emefiele’ ba tare da bayyana cewa shi ne gwamnan CBN ba, babban jami’in gwamnati wanda ke da matsayi mai matukar muhimmanci,” inji majiyar.  An ruwaito yana cewa.

Kotun ta ce kamata ya yi a rika bin irin wannan bukata da amincewar shugaban kasa saboda babban illar da ke tattare da tattalin arzikin Najeriya idan aka kama gwamnan CBN aka tsare shi.

Akwai zargin cewa yunkurin kame Emefiele na iya zama na siyasa duba da irin tasirin da sake fasalin kudin Naira da kayyade kudaden da ake kashewa zai iya haifar da sayen kuri’u a zaben 2023.

Tun a ranar Litinin din da ta gabata ne wasu kungiyoyin farar hula suka yi korafin cewa akwai wani shiri na sanya Emefiele da laifin ta'addanci da kuma tsige shi daga mukaminsa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN