Da Dumi-Dumi: Emefiele yana amfani da matsayinsa don 'azabtar' yan siyasa, Gwamnan Arewa mai karfin fada aji ya yi zargi


A wani abu da za a iya kwatantawa da cigaba mai ban mamaki, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya yi babban zargi kan gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele. Jaridar legit ta wallafa.

A cewarsa, Emiefiele yana kai wa yan siyasa hari ne da dokar kayyade adadin kudin da za a iya cire wa daga banki, Punch ta rahoto.

Har wa yau, Gwamna Finitiri ya ce an kawo dokar ne jim kadan bayan rashin nasara da Emefiele yayi a siyasa da ta zo karshe cikin gaggawa, kuma hakan ramuwar gayya ne saboda yana son tsananta talauci a cikin al'umma.

Ya ce:

"Me ke kawo talauci? Tsare-tsaren kudi. Duba wanda babban bankin kasa ke shirin aiwatarwa wanda ka iya kara jefa kasar cikin talauci, Babu wanda ke cewa kada a sauya tattalin arziki zuwa mara amfani da tsabar kudi ba.

"A dauki lokaci a yi shi dalla-dalla. Kada mu yi kamar wasu mutane sun so zama yan siyasa amma ba su samu dama ba, sannan su yi amfani da ofishinsu don hukunta yan siyasa."

Bugu da kari, Fintiri ya sake jadada kira ga cewa a mayar da kasar ta zama tarayya na ainihi. Ya kuma ce akwai bukatar a sauya tsarin fasalin kasar ta yadda jihohi da kananan hukumomi za su rika cin gashin kansu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN