An gano gawar wani dan kasuwa a cikin dakin Otel a Bauchi


An tsinci gawar wani dan kasuwa mai shekara 37, Mr Chukwunonso Chukwujekwu a unguwar Tudun Wada da ke Boi, karamar hukumar Bogoro a jihar Bauchi. Rahotun legit.ng.

Daily Trust Saturday ta tattaro cewa marigayi Chukwunonso dan asalin karamar hukumar Anambra East ne a jihar Anambra, amma yana zaune kuma yana kasuwanci a kauyen Boi.

Kafin rasuwarsa, babban sarkin Boi, Mallam Bala Likita ya nada shi sarautar Kaigaman Boi.

Wani mamba na Police Community Relations Committee, PCRC, a yankin, Joel Daniel ya ce mazauna garin sun shiga rudani kan yanayin mutuwarsa.

Daniel ya yi bayanin an tsinci gawar marigayin a otel bayan an kai wa PCRC da yan sandan Bogoro rohoton cewa ya bace, rahoton The Punch.

Da aka tuntube shi, kakkakin yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ya tabbatar da lamarin kuma ya ce kwamishinan yan sanda ya umurci a yi bincike kan mutuwarsa.

Yadda yan sanda suka gano gawar Mr Chukwujekwu

SP Wakili ya ce:

"Wata Mrs Grace Chukwujekwu, yar shekara 27, ta kai rohoto ofishin yan sanda na Bogoro a ranar 30 ga watan Nuwamban 2022 cewa mijinta, Mr Chukwunonso Chukwujekwu, ya bar gida don zuwa shagonsa a Boi amma tun lokacin bai dawo gida ba.

"Bayan ta shigar da rahoton, DPO na Bogoro ya jagoranci yan sanda sun fita bincike. Daga bisani, an gano gawarsa a wani otel da ke Tudun Wada a Boi, karamar hukumar Bogoro yana kwance a kasa kumfa na fita daga bakinsa."

Wakil ya kara da cewa an dauki shi an kai Babban Asibitin Bogoro inda likita ya tabbatar ya mutu kuma kwamishinan yan sandan ya umurci a yi binciken sanadin mutuwarsa yayin da ake cigaba da bincike.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN